Sakamakon wani tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar wasu mutane uku baya ga dukiyoyin miliyoyin nairori da aka salwantar sanadiyyar kone-konen da ya biyo baya a Karamar Hukumar Bwari, Ministan Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, Muhammad Musa Bello, ya sanar da kafa dokar hana fita a fadin Karamar Hukumar daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na asuba agogon Najeriya.
Bayan da Ministan na Birnin Tarayyar Najeriya ya yi shelar kafa dokar hana fita din, sai mai magana da yawun Ministan, Abubakar Sani, ya gaya ma Hassan Maina Kaina, wakilin Sashin Hausa Na Muryar Amurka cewa fada ne ya gaure tsakanin wasu matasa, wanda ya kai ga daba ma dayan wuka. Ya ce daga nan ne fa gari ya yamutse har tashin hankalin da ya biyo baya ya kai ga kone-konen kaddarori ciki har da babbar kasuwar Bwari.
Kakakin Rundunar ‘yan sandan Binrin Tarayya, Abuja ASP Anjuguri Manzah ya tabbatar da aukuwar lamarin. Amma ya ce an shawo kan lamarin. Manzah ya ce za a kaddamar da bincike saboda a gano musabbabin tashin hankalin a kuma hukunta duk mai laifi.
Ga dai wakilinmu Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:
Facebook Forum