Ofishin Firayim Ministan din yace wannan matakin na wucingadi ne da za’a ci gaba da aiki da shi har zuwa lokacinda aka kamalla gudanarda bincike akan ‘yanmajalisar.
An dauki wannan matakin ne dai a sanadin kukan da ministan tsaro na kasar Khaled al-Obeidi ya shigar a jiya Litinin na cewa Kakakin majalisar Salim al-Jabouri da wasu wakilan majalisar sun nemi suyi mishi yankan baya don yaki basu wasu manyan kwangiloli da suka nema na gwamnati. Daman ministan tsaron ya je gaban majalisar ne inda ya karbi tambayoyinta akan zargin almundahanar da akace tana gudana a cikin ma’aikatarsa.