A yayin da yake bayani ga manema labarai a karshen wata ganawa da Shugaban Majalissar CNSP a karshen mako, Shugaban sabuwar hukumar COLDDEF mai yaki da almundahana, Colonel Abdoul wahid Djibo, ya sanar cewa shi da mukarrabansa suna samun nasarori a aiyukan kwato kudaden da aka wawure.
Ya ce bitar wadanan aiyukan a halin yanzu na nunin sun kwato sama da million 15,000 na cfa, abin da ya yi matukar kayatar da shugaban kasa har ma ya kara jaddada basu goyon baya inji shi.
Shugaban hukumar ya ce turjiyar da suka fuskanta ita ce wace ke da nasaba da HALCIA domin a cewar sa ita wannan tsohuwar hukumar yaki da cin hanci ta lalata dukkan bayanan binciken da ta gudanar a zamaninta, in ban da wasu takardun koke koken da ta damka masu.
Sai dai a wata rubatacciyar sanarwar da suka aike wa manema labarai, kwamishinonin tsohuwar hukumar ta HALCIA sun yi watsi da wannan zargi da suka kira marasa tushe balle makama.
A cewarsu dukkan bayanan da ake magana akansu suna nan a hannu kuma babu wani abu da aka lalata.
Hakazalika, sabuwar hukumar ta COLDDEF ba ta taba nuna bukatar samun wasu bayanai ba in ban da rahotannin da ta bukaci ta samu daga HALCIA, kuma aka ba ta inji sanarwar hadin guiwar kwamishinonin tsohuwar hukumar HALCIA.
Tuni ‘yan fafutika suka fara bayyana takaici akan faruwar wannan dambarwa da suke ganin ba abin da za ta samar face haddasa koma baya a yakin da aka kadammar da barayin dukiyar kasa.
Shi ma Shugaban kungiyar FCR Souley Oumarou, ya nuna rashin jin dadin wannan cece kuce, koda yake a cewar sa alama ce ta gazawar sabuwar hukumar a yakin da aka dora mata alhakin aiwatarwa.
Cin hanci da almudahana na daga cikin manyan matsaloli da ake ayyana wa a matsayin dalilan da ke dabaibaye tattalin arzikin Nijar da ci gaban al’ummarta.
A baya dukkan hukumomin da aka dorawa wannan nauyi sun yi fama da turjiya walau ta ‘yan siyasa ko daga mahukunta abin da ya sa aka wajabta wa jami’an da abin ya shafa rantsuwa kan littafi mai tsarki domin tabbatar da adalci da gaskiya.
Domin karin bayani saurari rahotan Souley Moumouni Barma.
Dandalin Mu Tattauna