Bana hukumomin kasar Saudiya sun ce sabili da bullar cutar ta ebola duk wani maniyatta sai an tabbatar da koshin lafiyarsa kafin ma a barshi ya shiga kasar.
Matsayin kasar Saudiya yasa mahukuntan jihohin Taraba da Adamawa suka dauki kwararan matakai domin ganin cutar bata shafi wani maniyata ba daga jihohin.
Malama Zaliyaha Manzo jami'ar hulda da jama'a ta hukumar alhazan jihar Adamawa ta bayyana irin shirin da suka yi bana. Tace bayan an tara maniyata a sansaninsu ne za'a fara tantancesu. Ta umurci maniyatan da su kula da duk wani zazzabi da suke fama dashi kafin a tarasu wuri daya. A lokacin likitoci zasu binciki lafiyarsu. Duk wanda aka samu da wani zazzabi likitoci zasu wareshi gefe daya domin a kara yi masa bincike.
Dangane da kujerun zuwa hajjin jami'ar tace za'a bi yadda suka fara biyan kudi ne, wato wadanda suka fara biya su ne za'a fara basu kujeru har a kai na karshe. Wadanda suke baya can da wuya su samu.
Kamar jihar Adamawa a jihar Taraba ma hukumar alhazai ta jihar ta dauki matakai irin na Adamawa. Alhaji Habibu Almaki babban sakataren hukumar alhazan jihar Taraban yace sun buga takardar da zasu baiwa maniyatan da sibitocin da zasu je domin a gwadasu koda akwai mai dauke da cutar ebola. Ya kira alhazan su hakura da duk matakan da aka dora masu.
Ita ma hukumar alhazan Najeriya ta kira hukumomin alhazan jihohi da su kula da alhazansu. Alhaji Zakari Al'umma jami'in hukumar mai kula da jihar Adamawa yace hukumomin jihohi su bada karfi wurin fadakar da alhazai su fahimci ainihin mahimmancin abun da zai kaisu aikin hajji.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.