Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Garambawul A Majalisar Minisoticn Nijar.


Shugaban Kasar Nijar Mahammadou Issoufou
Shugaban Kasar Nijar Mahammadou Issoufou

Dangantakar dake tsakanin jam’iyyar MPN Kishin Kasa da jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulkin kasar ta tabarbare lamarin da ya jawo garambawul din.

Garambawul din ya shafi ministoci biyu daga jam’iyyar MPN Kishin Kasa da minista daya daga jam’iyyar RDP kamar yadda sanarwar da sakataren gwamnatin kasar ya fitar cikin daren jiya Laraba tayi bayani.

A cewar sakataren, bayan da Firayim Ministan kasar ya zo da sunayen wasu mutanen da yake ganin sun cancanta, Shugaban Kasa Mahammadou Issoufou ya nada Kalla Hankurau na PNDS Tarayya a mukamin ministan harkokin waje wanda ya maye gurbin Ibrahim Yacuba na jam’iyyar MPN Kishin Kasa. Kazalika shugaban ya nada Salisu Mahamma na RDN Fasaha, ya maye gurbin ministar watsa labarai Kubura Abdullahi ta MPN Kishin Kasa.

Haka kuma shugaban kasar ya nada Sanusi Alhaji Samro na RDP Jama’a a, mukamin ministan ilimi a matakin sakandare,wanda ya maye gurbin wani kusan jam’iyyar RDP Sani Abdulrahaman.

Tun a yammacin jiya Laraba shugaban jam’iyyar ta MPN Kishin Kasa Ibrahim Yacuba ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa Firayim Ministan kasar Birgi Rafini ya shaida masa cewa Shugaban kasa yace baya bukatarsa a cikin gwamnatinsa, dalili ke nan da ya rubuta takardar murabus kafin daga bisani Kubura Abdullahi ta bi sawunsa, matakin da tuni ya samu karbuwa a wurin mayakan jam’iyyar MPN Kishin Kasa irin su Habila Rabiu.

A cewarsa yanzu sai su duba su ga me ya sa Shugaba Mahammadou Issoufou yace baya son ganin shugabansu Ibrahim Yacuba a gwamnatinsa. Ya kara da cewa su basu shiga gwamnati ba tun can farko domin a yi anfani dasu a yaudari jama’ar kasar.

Jam’iyyar MPN Kishin Kasa, wacce ta zo ta hudu a zaben kasa na 2016 tun makon jiya ta fitar da wata sanarwa inda ta ce ta fara kosawa da halin wasa tare da ci banban da jam’iyyar PNDS ke nuna mata musamman a zabukan dake tafe a shekarar 2021 inda ta ce PNDS ta yi kane-kane a shirye shiryen zaben.

Sai dai mai magana da yawun PNDS Tarayya ya ce a cikin kawancen da suke tafiya tare, akwai jam’iyyun da suka fi MPN karfi kuma da su ne suke muamala.

Dama tun farko wasu jaridu na cewa ana fuskantar baraka tsakanin MPN da PNDS lamarin da ya sa shugaban kasa ya daina zuwa balaguro da ministansa na harkokin waje Ibrahim Yacuba.

Souley Mummuni Barma nada karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG