Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar MPN Ta Fice Daga Kawancen Jam’iyyun Dake Mulkin Kasar Nijar


Taron Jam'iyyar MPN Kishin Kasa a karkashin shugabancin Ibrahim Yacuba
Taron Jam'iyyar MPN Kishin Kasa a karkashin shugabancin Ibrahim Yacuba

A taron manema labarai shugaban jam’iyyar MPN Kishin Kasa Ibrahim Yacuba ya tabbatar da ficewar jam’iyyarsu daga kawancen jam’iyyun dake mulkin kasa saboda wai kundun tsarin zabe da babbar jam’iyyar kasa PNDS Tarayya tayi kane-kane a kai zai haifar wa kasar matsaloli nan gaba idan har ba’a gyara ba

Shugaban jam’iyyar MPN Kishin Kasa Ibrahim Yacuba kuma tsohon ministan harkokin kasashen waje na Nijar har ya zuwa jiya da ya bar aiki ya yiwa Muryar Amurka karin bayani akan ficewarsu daga kawancen jam’iyyun dake mulkin kasar.

A cewarsa duk lokacin da aka yi zabe sulhu a keyi da mutane amma kundun tsarin zabe da gwamnatin kasar ta nace a kai , wai bashi da niyyar yin sulhu. Baicin haka kundun ya kunshi wasu matakai da zasu kawowa kasar matsala nan gaba. Inji Malam Yacuba kwanciyar hankali a kowace kasa ya ta’allaka ne akan yaddar da jama’ar kasar ke dashi a zaben sugabanninsu. Sun kira a yi sulhu, a samar da kundun zaben da kowa ya yadda dashi domin bunkasa Dimokradiya.

Jam’iyyar ta ce daga rana ta jiya da ministocinta suka ajiye mukamansu, ta fita daga gwamnati kuma bata marawa gwamnatin kasar baya.

Ficewar jam’iyyar ba wargi ba ne ba kuma da gangan suka yi ba saboda jagoranci babban nauyi ne da al’umma ke bayarwa Allah kuma zai tambayesu abun da suka yi da amanar da aka basu, inji Yacuba.

Sai dai wani jigo a jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki Alhaji Asumanu Muhammadu ya ki yayi magana amma ya bada shawarar a jira nan gaba a ji bahasin koli na jam’iyyarsu

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG