ACCRA, GHANA - Tsohon sbugaban ya kuma gargadi jami’an zabe da su daina nuna wariya ga mazauna Zango, musamman domin sunayensu.
Zango wani mazauni ne ko matattara na al'ummomi masu matsakaicin karfin arziki daga Arewaci da kudancin Ghana, da kuma mafi yawanci, baki da suka yi gudun hijira daga kasashen Afirka ta Yamma shekaru da dama da suka gabata.
Tsohon shugaban kasa John Mahama, a wajen taron masu ruwa da tsaki da jam’iyar NDC reshen Zango ta shirya domin jin kukan mazauna Zangunan Accra, don a kara cikin manufofin jam’iyar kafin zaben 2024, ya ce matsalar da ‘yan Zango ke fuskanta na banbanci da wariya da ake nuna musu a wajen yin katin zabe da ake gudanarwa yanzu bai dace ba, domin tarihi na nuni da cewa, ‘yan Zango suna cikin Ghana shekaru da dama kafin Ghana ta samu ‘yancin kanta.
Domin haka idan aka kira sunan mutum,an gane kamar Fulani ne, ko Zabarma ne ko Bahaushe ne sai a ce ba ‘yan Ghana bane. Amma idan aka dubi tarihin kasar, ya ce kakanninmu sun zo nan tun karni na goma sha hudu, don haka kada a nuna babanci domin sunan mutum ya kasance haka, ace ba za a iya yi musu rijista ba.
Wasu masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun bayyana bukatunsu da suke da burin a cika musu. Kamar daya daga cikin wakilin sarakunan Zango, Sarkin Zabarmawan nima, Sai’du Luis ya ce, Majalisar Sarakuna na da fili da suka ajiye domin gina makaranta, suna bukatar jam’iyar ta gina musu makarantar idan ta hau mulki.
Jakadiyar Sarkin Hausawan Accra a nata bangaren ta ce a kula da matasa sannan kuma a magancewa Musulmai matsalar wajen ajiye gawa; ta kuma ce a yi shi yadda ya dace da Musulunci.
Taron ya samu halartar limamin limamai na Ghana, Dr. Usman Nuhu Sharubutu, da limamin Ahlul Sunna wal Jama’a, Shaikh Umar Ibrahim, da wakilcin Majalisar Sarakunan Zango da Kungiyoyin fararen hula daban-daban na Zongo.
Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullah:
Dandalin Mu Tattauna