Gwamnatin jamhuriyar Congo tace bular anobar Ebola a gabashin kasar ta kashe mutane arba’in da tara tun farkon wannan wata, kuma kungiyar lafiya ta duniya tace ana fargaban samun karuwar wadanda suka kamu da cutar.
Karuwar yawan wadanda cutar ta kashe sannun kan hankali da kuma tsoron da ake ji cewa kimamin mutane dubu biyu sun kusanci wadanda suka kamu da cutar, ya dada cakuda al’amurran kasar, wadda tuni take fama da tarzoma da kuma rashin sanin tabbas akan makomar harkokin siyasa a kasar
A ranar daya ga watan nan na Agusta aka bada sanarwar bullar anobar a lardin Kivu ta arewa, a barkewar cutar ta baya bayan har ta kashe mutane arba’in da tara daga cikin mutane casa’in da aka bada rahoton sun kamu da cutar.
Facebook Forum