Ana zaton shi matashin zai tsallaka da tabar ne zuwa kasashen waje dake makwaftaka da Najeriya.
Jihar Borno dake makwaftaka da kasashen Chadi da Kamaru da Niger yasa akan samu aukuwar alamura da dama kamar safara miyagun kwayoyi da kuma abun da ya danganci tsaro. Ranar 20 ga watan Agusta nan ce rundunar 'yansandan ta kame babbar motar kirar marsandi dake dauke da buhunhunan ganyen tabar wiwi har 248. Kowane buhu yana dauke da kunshin tabar 20.
Motar ta fito ne daga garin Akure na jihar Ekiti tana kokarin tsallaka iyaka daga garin Maiduguri ta shiga wata kasar kafin dubunta ta cika. Rundunar ta gurfanar da matashin ne dan shekara 35 da haihuwa mai suna Kole Alade dake da buhuhuwan wadanda aka yi masu nadi na musamman kamar burodi aka kuma lullubesu da abincin yara da nufin badda kama.
Mai magana da yawun rundunar 'yansandan DSP Gideon Jibrin ya shaidawa Muryar Amurka yadda suka samu nasarar kame matashin.
Matashin ya musanta mallakar tabar wadda yace ba tashi ba ce. Yace shi makaniki ne kuma an kirawoshi ne ya gyara motar lokacin da ta lalace. Bayan ya gyara motar aka rokeshi ya shiga motar zuwa garin Maiduguri inda za'a biyashi hakinsa kudi nera dubu goma. Yace shi bai taba zuwa garin Maiduguri ba.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.