Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari, Mahamadou Issoufou Sun Tattauna Kan Harin Nijar


Shugaban Najeriya, Buhari, (hagu) da Shugaban Nijar, Issoufou, (dama) (Hoto: Shafin Instagram)
Shugaban Najeriya, Buhari, (hagu) da Shugaban Nijar, Issoufou, (dama) (Hoto: Shafin Instagram)

“Najeriya za ta taimakawa duka makwabtanta wajen yaki da ayyukan ta’addanci.” Shugaba Buhari ya ce.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya jajinta wa takwaran aikinsa na Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou da al’umar kasar kan hare-haren da aka kai a wasu yankunan kasar.

A ranar Talata Buhari ya kira Issoufou ta wayar tarho inda shugabannin biyu suka amince su kara tsaurara matakan tsaro a yankunan kasashen biyu da ke makwabtaka da juna don dakile ayyukan kungiyoyin Boko Haram da na ISWAP a yankin Hamadar Sahara da na Sahel.

Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu Buhari , Nigeria, da Najeriya.

“Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda suka mutu da al’umar Jamhuriyar Nijar.” In ji wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar dauke da sa hannun kakakinsa Malam Garba Shehu.

A ranar Lahadi aka kai hari a wasu kauyukan jihar Tahou inda aka kashe mutum 137, harin da Buhari ya yi Allah wadai da shi.

Shugabannin kasashen yankin Sahel
Shugabannin kasashen yankin Sahel

“Najeriya za ta goyi bayan duka makwabtanta wajen yaki da ayyukan ta’addanci,” sanarwar ta kara da cewa.

Nijar, Mali da Burkina Faso na fama da matsalar hare-haren ‘yan ta’adda a kan iyakokinsu, lamarin da kan kai ga asarar dumbin rayuka da dukiyoyi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe mutum sama da 290 a tsakanin watan Janairu zuwa Maris a hari daban-daban da aka kai a tsakanin Tahoua da Tillabery.

Masu lura da al’amura na nuni da cewa, batun tsaro na daga cikin babban kalubalen da zababben shugaban kasa Bazoum Mohamed zai fuskanta idan ya karbi mulki a ranar 2 ga watan Afrilu.

Zai maye gurbin shugaba Issoufou wanda yake shirin kammala wa’adinsa na biyu.

Baya ga yankin Tahou da Tillabery, wani yanki da ke fama da matsalar tsaro shi ne na Diffa inda mayakan Boko Haram daga Najeriya kan shiga su yi barna.

XS
SM
MD
LG