A jihar Kebbi kungiyar kwadago ta kawo karshen yajin aikin da ta soma bayan ta shiga rana ta biyu.
Rashin jituwa da gwamnatin jihar ya kaiga kungiyar shiga yajin aikin. Badakalar ta soma ne a yammacin ranar Talatan nan, ranar da wa'adin da ta baiwa gwamnatin domin biya mata bukatunta har guda takwas ya cika ba tare da samun wani bayani ba daga gwamnatin jihar. Rashin ji daga gwamnatin yasa kungiyar ta shiga wani yajin aikin "sai baba ta gani" daga ranar Laraba.
Sadiq Sambo Ka'oje shgugaban kungiyar kwadagon jihar Kebbi ya bayyana korafe-korafensu. Yace suna da matsaloli akan samun albashi musamman na dubu goma sha takwas. An fara biyan kudin amma babu wata takardar doka da zata bashi karfi domin a biya albashin a duk fadin jihar. Ban da haka idan a ka karawa mutum girma a wurin aiki ba za'a sa ga albashi ba. Sabili da haka da wasu matsalolin har guda takwas sun rubutawa gwamnati suka kuma bada wa'adin satin uku gwamnati ta dubi matsalolin. Rashin yin abun da yakamata a bangaren gwamnati yasa suka fara yajin aikin.
Gwamnatin jihar Kebbin ta gaggauta daukan mataki akan lamarin tun a ranar farko da kungiyar ta shiga yajin aikin. Bayan kwashe yini daya a teburin sasantawa da kungiyar an samu daidaito tare da raftaba hannu a yarjejeniyar biyan bukatun ma'aikatan.
Biyo bayan jarjejeniyar da aka cimma shugaban kungiyar kwadagon ya bayar da sanarwar janye yajin aikin jiya. Yace sun zauna da gwamnati sun kuma amince 'yan kwadagon nada gaskiya sabili da haka sun sa hannu su biya bukatunsu.
Shugaban ma'aikata na jihar Kebbi Buhari Haliru Jega ya tabbatar da cimma matsayar da kuma kudurin gwamnati na biyan bukatunsu.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.