WASHINGTON DC - Majiyar wacce ta nemi a sakaya sunanta tace, an yanke shawarar ajiye fitilar Olympic din a dandalin 'yan yawon shakatawa na birnin ne makonni da dama da suka gabata.
Majiyar ta kara da cewar, an zabi lambun tuileries ne tunda fari saboda saukin isarsa ga al'umma.
A cewar majiyar, akwai rade-raden cewar akwai yiyuwar dora fitilar akan husumiyar "Eiffel Tower", inda masu shirya wasannin suka yi tunanin ajiyeta a farfajiyar louvre: gidan adana kayan tarihi mafi girma a duniya.
Majiyar tace, Lambun Tuileries yanki ne da za'a iya tsarewa cikin sauki. Za'a samar da jami'an tsaro tsawon sa'o'i 24 domin tsare fitilar sa'annan al'umma zasu iya hangota daga ko'ina saboda tudun da aka yiwa hanyoyin dake cikin lambun.
Har yanzu ba'a bayyana sunan mutumin da aka yiwa alfarmar kunna fitilar ba, kuma ba'a bayyana tsare-tsaren bikin bude wasannin da a karon farko zai gudana a wajen filin wasa ba.
Masu shirya wasannin sun sha alwashin mayar da Olympic din birnin mafi kasaita da aka taba yi cikin shekaru 100.
Dandalin Mu Tattauna