Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NSCDC Ta Kama 'Yan Fashi Da Makami Har 33


Hukumar Tsaron Al’umma
Hukumar Tsaron Al’umma

Hukumar tsaron al’umma ta Civil Defence a jihar Nasarawa ta kama gaggan ‘yan fashi 23 da take zargi da kaurin suna wajen fashi da makami, da sace kayayyakin ofisoshin gwamnati.

Kwamandan rundunar Civil Defence a jihar Nasarawa, Muhammad Gidado Fari, yace gungun ‘yan fashin sun dade suna cutar al’ummar jihar ta Nasarawa.

A hirar su da wakiliyar Muryar Amurka shugaban gidan rediyon tarayya na Precious FM dake Lafia, Musa Abdullahi yace ‘yan fashin sun tabka musu barna a ofishin.

Tuni dai hukumar ta Civil Defence ta gurfanar da wadanda take zargin a gaban kotu.

Ga cikakken rahoto daga wakiliyar muryar Amurka Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG