An fara gasar cin kofin kwallon Kafa ta duniya ta shekarar 2018 wace kasar Rasha ta dauki nauyi.
An fara gasar ne tsakanin mai masaukin baki kasar Rasha da takwararta ta Saudi Arabia. a filin wasa na Luzhniki dake birnin Moscow. da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi.
Bayan haka Kasar Amurka. da Canada da kuma Mexico sune aka zaba a matsayin kasashen da zasu dauki nauyin gasar cin kofin kwallon Kafa na duniya wanda za a yi a shekarar 2026.
Kasashen dai sun samu nasarar daukar wasanne bayan da sukayi takara da kasar maroko, wacce itama ta nema da abata.
Mambobin 200 a cikin 211 zababbu daga hukumar kula da kwallon Kafa ta duniya Fifa suka kada kuri'unsu don zaben kasar da za'ayi gasar ta 2026, inda kasahen Amurka, Mexico, da na Canada suka samu kuri'u 104 a cikin 200 da aka jefa.
An gudanr da zaben ne a Birnin Moscow dake kasar Rasha a ranar laraba 13/6/2018. Gasar ta cin kofin duniya da za'ayi a 2026 zata kasance mafi girma wadda ba'a taba yin kamarta ba a tarihin gasar.
A wannan gasar ne hukumar fifa ta amince da cewa kasashe 48 ne zasu fafata a maimakon 32 da ake yi, jimillar wasanni 80 a cikin kwana 30 cif.
Facebook Forum