Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastan Za Ta Janye Takardar Izinin Wucin Gadin Fiton Kaya A Nijar


Shugaban Nijar, Bazoum Mohamed (Instagram/PNDS Tarayya)
Shugaban Nijar, Bazoum Mohamed (Instagram/PNDS Tarayya)

Kungiyoyin ‘yan kasuwar Jamhuriyar Nijar sun bayyana farin ciki bayan da shugaban hukumar Douane ya umurci ma’aikatansa su dakatar da matsawa ‘yan kasuwa game da takardar izinin wucin gadin fiton kaya.

Wannan takarda dai ita ce da aka saba karba a can baya akan hanyoyin cikin gida to sai dai sun ce zasu bi diddigin wannan mataki don ganin ba a sake komawa ruwa ba.

Yawaitar korafe korafen ‘yan kasuwa a game da takardar fiton kaya ta wucin gadi wato Passavant da kuma irin yadda tsarin ke tarnaki ga harakokin kasuwanci ya sa shugaban hukumar Douane aika wasika ga ma’aikatansa na jihohi wace ta hanyarta ya dauki matakin soke wannan tsari.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa Alhaji Hatimou Sama’ila mai aya na daga cikin wadanda suka yi gwagwarmayar ganin an sami wannan sassauci.

Shugaban kungiyar SIEN ta ‘yan kasuwar dake shigo da kaya daga waje Alhaji Yacouba Dan Maradi wanda ya jima cikin wannan fafitika ya yaba da wannan matakin na shugaban ma’aiaktar Douane to amma ya ce akwai bukatar duba wasu matsalolin na daban dake addabar ‘yan kasuwa akan hanyoyi.

Ganin yadda sau da yawa ana fuskantar tufka da warwara wajen gudanar da ayyukan hukuma a Nijar ya sa shugabannin ‘yan kasuwa suka kudiri aniyar bin diddigin wannan sabon mataki domin tabbatar da cewa ma’aikatan kan hanya ba su yi gaban kansu ba a wannan karon.

Matakin wanda ya fara aiki a take yanke wata hanya ce ta samar da sassauci ga ‘yan kasuwar dake isar da kaya daga birnin Yamai zuwa sauran sassan kasa musamman wadanda ake shigo da su ta tashoshin jirgin ruwa yayinda ta wani bangare abin ke zama wata hanyar magance cin hancin da wannan tsari ka iya haddasa wa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni barma:

Matakin Janye Takardar Izinin Wucin Gadin Fiton Kaya A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00


XS
SM
MD
LG