Gwamnatin jihar Taraba, daya daga cikin jihohin da suka kafa dokar hana kiwo a Najeriya tace ba gudu ba jada baya wajen soma aiwatar da wannan dokar duk da korafe-korafen da ake yi game da wannan sabuwar doka.
Rahotanni dai sun bayyana cewa gwamnatin jihar tuni ma ta dauki zaratan jami’an hana kiwon da za’a yiwa lakabi da yan Marshal, kuma an dauko goma-goma daga matakan mazabun anguwanni wato wod-wod da suka kai dubu daya, inda za’a basu horo na musamman kafin bazasu a kananan hukumomin jihar goma sha shida.
Da yake karin haske ga manema labarai bayan wani taron sirri da sarakunan gargajiyan jihar, mataimakin Gwamnan jihar Taraban, Haruna Manu, yace dokar da zata soma aiki daga wannan rana ta 24 ga watan Janairu kuma ya samu amincewar sarakunan gargajiya, yayin da za’a soma aiwatarwa daki-daki.
Hon. Ibrahim Bappa Waziri tsohon jami’in tsaro ne kuma tsohon dan majalisar dokoki, yace kafin kafa irin wannan dokar akwai matakan da ya kamata a dauka. Kamar Bappa Waziri shima wani masanin Dokta Agoso Bamaiyi, yace ai wasu dokokin da ake fadi na burtali ko hurumin dabbobi, akwai bukatar duba su don tafiya da zamani.
Facebook Forum