Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisun Tarayyar Najeriya Sun Rena Umarnin Kotu, Ko Dai Da Magana?


Birnin trayyar Abuja.
Birnin trayyar Abuja.

Senata David Mark Da Aminu Tambuwal sun rena umarnin kotu a rikicin CPC?

David Mark da Tambuwal sun rena umarnin kotu a rikicin ‘yan CPC a majalisa?

Rikicin da ake yi tsakanin ‘yan jam’iyyar CPC daga jihar katsina daga bangaren Senata Lado da Aminu Bello Masari, yanzu zai hada da shugabannin majalisun tarayyar duka biyu.

Domin bangaren senata Lado, wadanda kotun daukaka kara ta tarayya ta goyi bayansu a hukuncinda ta yanke ranar daya ga watan Nuwamban nan, suna zargin Senata David Mark, da Aminu Tambuwal da laifin rena umarnin kotu. Kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke tace sune ya kamata su dare kan kujerun nan 10 dake majalisar dattijai data wakilai, amma shugabannin majalisun biyu da akawunansu, sun ki barinsu su kama aiki. Daya daga cikin 'yan majalisar senata Ahmed Sani Store shine ya bayyanawa wakilinmu Umar Farouk Musa haka a tattaunawarsu a Abuja.

Maimakon haka suka ce da su sai su tafi hukumar zabe su kawo takardar shaidar da hukumar zabe ta basu cewa sune suka lashe zabe.

Senata Ahmed Sani Store, wanda shi da sauran wakilan suka kira taron manema labarai kan wannan takaddamar sun bayyana cewa zasu koma kotu domin neman ta tilastawa shugabannin majalisun su mutunta umarnin shari’a.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Jimmy Bada, ta amince da shari’ar da karamar kotu ta yanke a rikicin, ta kuma kori karar da wakilan CPC a bangaren Aminu Bello Masari suka shigar wadanda sune ahalin yanzu suke rike da kujerun CPC a majalisun daga jihar katsina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG