Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar DSS Ta Sako Tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa


Abdulrasheed Bawa, tsohon shugaban hukumar EFCC
Abdulrasheed Bawa, tsohon shugaban hukumar EFCC

'Yan uwa da abokan arziki sun yi dafifi su na ta murnar sako shi. Alhaji Rabiu Gada na daga cikin iyayen Bawa wanda kuma ke kan gaba wajen ganin an sako shi. Ya ce, "An yi bincike ba a samu wani laifi ba, kuma mun yi murna sama da tunanin da ba ka sani ba."

ABUJA, NIGERIA - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta saki tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Abdulrasheed Bawa, biyo bayan tsawaita zamansa na tsawon sama da kwanaki dari. Tun a watan Yuni aka tsare Bawa, lamarin da ya wakana bayan dakatarwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi mashi daga ofishinsa.

Kamar yadda Daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey, ya bayyana a baya, akwai zarge-zarge da dama da ake yi wa Bawa, wanda ya hada da zargin Bello Matawalle, tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma karamin ministan tsaro, inda ya ce Bawa ya bukaci a ba shi cin hancin dala miliyan biyu, lamarin da Bawa ya musanta.

Peter Afunanya, kakakin hukumar DSS ne ya tabbatar da matakin sakin Bawa, wanda ya bayyana cewa Bawa ya samu ‘yancinsa a ranar Laraba. Tuni dai wani faifan bidiyo da ke nuna haduwar Bawa da iyalansa ya yadu a kafafen sada zumunta.

Ga lauya Barista Modibbo Bakari wanda ya ke da masaniya kan binciken da a ka yi wa Bawa ya ce rashin bayanai tun farko da bai yi ba ya kawo jinkirin sake shi ko gurfanar da shi gaban kotu.

Idan dai ba a manta ba, kafin a sake shi, Bawa ya fuskanci binciken da jami’an DSS suka yi masa a gidansa da ofishinsa da ke babban birnin tarayya, har ma ya shafe bikin Sallar layya a hannun jami’an tsaro na farin kaya wato DSS.

Sai dai duk da sakin nasa har yanzu jami’an DSS ba su bayyana irin abubuwan da suka gano na tuhume-tuhume da ake yi masa ba, lamarin da ‘yan Najeriya har yanzu su ke dako su ji da kuma makomar tsohon shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa.

-Yusuf Aminu Yusuf

Ga kuma karin bayani daga rahoton Nasiru Adamu El-Hilaya:

Hukumar DSS Ta Sako Tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG