Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hattara Barayin Waya


Wayar hannu ta zamani
Wayar hannu ta zamani

An samu raguwar masu satar wayoyin hannu tun da kamfanonin dake kera wayoyin zamani suka bude wata dama ta amfani da wani abu da ake kira “kill switch” wajen nemo inda waya take da goge bayanan dake cikin waya a duk inda kake, harma da ruguza wayar domin kada ta kara yin amfani.

A baya, satar wayoyin hannu ta yawanta inda wasu barayi ke warcen wayoyin a hannun mutane. Amma yanzu haka an fara maganin su, wani nazari da aka gudanar an gano cewa a shekarar da ta wuce kadai an saci wayoyin mutane a Amurka sama da miliyan biyu, mutane sama da miliyan uku kuma sun yarda wayoyin su, haka a shekara ta 2013 sama da wayoyi miliyan uku aka sace.

Masu hayoyin hannu na iya amfani da fasahar “kill switch” su goge duk abinda ke cikin wayoyin su alokacin da suka batar dasu ko aka sace musu. A shekara 2013 ne wasu lauyoyi masu gudanar da ‘kara a Amurka suka yi kira ga kamfanonin wayoyin zamani da su kirkiro fasahar da zata baiwa masu amfani damar kashe ko goge bayanansu alokacin da aka sace musu wayoyin su domin hana ‘barayi amfanin da bayanan, ko sayar da wayoyin a kasashen waje.

Kamfanin Apple dai na gaban takwarorin sa wajen kirkirar wannan fasaha, a shekara ta 2013 ya fara amfani da wani afilikashin mai suna “Find My iPhone” wato nemo min waya ta, a dalilin haka ne ma’aikatar ‘yan sanda suka fitar da rahotan raguwar satar wayar iPhone.

XS
SM
MD
LG