Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutum 25 Tare Da Jikkata 53 A Hanyar Kano Zuwa Zaria


Hatsarin mota
Hatsarin mota

A cewar Kwamandan Shiyyar Kano na Hukumar FRSC, “binciken farko ya nuna akwai yiyuwar cewar tsananin gudu ne ya sa tirelar ta kwace daga hannun direbanta”.

Hatsarin motar da ya faru akan gadar Keyawe ta Dangwaro da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Zaria ya hallaka mutum 25, tare da jikkata wasu 53.

Shiyyar Kano na Hukumar Hana Afkuwar Hadura ta Najeriya (FRSC), ta tabbatar da fkuwar mummunan al’amarin da ya faru da kimanin karfe 3":30 na asubahin Litinin.

Kwacewar wata babbar mota kirar tirela saboda gudun wuce sa’a ne ya sabbaba hatsarin. Kuma rahotannin sun bayyana cewar tirelar na dauke ne da mutane 90, abin da ya ta'azzara yawan mace-mace da jikkata.

Sai dai, an yi sa’ar kubutar da mutum 12 ba tare da ko rauni ba.

A cewar Kwamandan Shiyyar Kano na Hukumar FRSC, “binciken farko ya nuna akwai yiyuwar cewar tsananin gudu ne ya sa tirelar ta kwace daga hannun direbanta”.

Nan take bayan afkuwar jami’an Hukumar ta FRSC da hadin gwiwar ‘yan sandan da sauran hukumomin ba da agaji suka kaddamar da aikin ceto da ba da agajin gaggawa.

Kayayyakin da aka samu a wurin da hatsarin ya afku sun hada da babura 6 da wayoyin hannu 10 da dabbobi (tumaki da awaki) da buhuhunan masara da kudi Naira dubu 4, wadanda tuni aka mikasu hannun ‘yan sanda.

Hukumar ta FRSC ta bukaci direbobi su kiyaye ka’idojin hanya dana tuki domin kare afkuwar bala’o’i akan titunan Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG