Mutane 31 ne suka hallaka a Mali a ranar Talata wasu 10 kuma suka jikkata bayan wata motar safa da ke kan hanyar zuwa Burkina Faso ta fado daga wata gada da ke kudu maso gabashin kasar, in ji ma'aikatar sufurin kasar.
Ta kara da cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 5:00 na yamma (1700 GMT) a wata gada da ta ratsa kogin Bagoe. "Wata bas...da ta tashi daga Kenieba zuwa Burkina Faso ta fado daga wata gada. Mai yiwuwa motar ce ta kwace wa direban," in ji ma'aikatar a cikin wata sanarwa.
Ana yawan samun hadurran ababen hawa a kasar Mali, inda manyan tituna da kuma ababen hawa ba su da kyau.
A farkon wannan watan mutane 15 ne suka mutu sannan 46 suka jikkata bayan wata motar safa da ta nufi Bamako babban birnin kasar ta yi karo da wata babbar mota a tsakiyar kasar Mali.
Dandalin Mu Tattauna