Tsohon gwamnan yankin Maradi Malam Ali Chaibou Maazou ya ce irin wannan hari sabon abu ne a kasar Nijer
WASHINGTON, DC —
Aliyu Mustapha Sokoto ya tattauna da tsohon Gwamnan yankin Maradi Malam Ali Chaibou Maazou wanda yanzu haka ya mallaki gidan rediyo mai zaman kan shi a Arlit, sun tattauna a kan hare-haren ta'addancin da aka kai kasar jamahuriyar Nijer, a Agadas da kuma Arlit. Tsohon Gwamnan yankin na Maradi Malam Ali Chaibou Maazou ya ce hakika ba a saba ganin irin wannan abu a kasar Nijer ba, ya ce bakon abu ne. Ya ce a yi addu'a Allah Ya kiyaye amma abun da aka yi a Arlit musamman abu ne wanda ya tayar da hankula saboda ba a saba ganin irin haka ba. Aliyu Mustapha Sokoto ya tambayi Malam Ali Chaibou Maazou ko a ganin shi me ya janyowa Nijer wannan al'amari, sai ya amsa da cewa: