Ministan Tsaron Nijar ya tabbatar da kashe mutanen da hannun dakarun Faransa a farmakin. Akwai rahotonnin da ke cin karo da juna game da halin da mutanen da ‘yan bindigar su ka yi garkuwa da su.
‘Yan bindiga masu tsattsauran ra’ayin Islama sun kai hari kan barikin a garin Agadez da kuma kamfanin hakar ma’adanin Uraniyum mallakin Faransa a Arlit a lokaci guda jiya Alhamis da safe. Harin da aka kai barikin sojojin ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 20, wadanda akasarinsu sojojin Nijar ne.
Kungiyar tsattsauran ra’ayin Islama ta MUJAO da ke Mali ta dau alhakin kai harin, kamar yadda shi ma tsohon shugaban kungiyar al’kaida shiyyar arewacin Afirka Mokhtar Belmoktar shi ma ya yi ikirari.
Sun ce harin martani ne ga jagorancin da kasar ta Faransa ke yi a yakin da ake yi da mayaka masu tsattsauran ra’ayin Islama a Mali.