Masana fannin ilimi a taron kasa suna ganin yakamata a yi anfani da ilimi a yaki jahilci da lalaci da talauci. Masanan suna nanata mahimmancin ilimi domin fannin ya samu kashi saba'in cikin dari na kuri'un 'mahalartar taron lamarin da suke gani zai taimakawa ilimi ya samu kaso mai tsoka a kasafin kudin kasar. Idan hakan ya faru fannin ilimi zai samu kayan aiki da suka dace ya kuma samu ingantuwa da biyan malamai yadda ya kamata.
Tsohuwar ministar ilimi Farfasa Rukayatu Rufa'i tace duk kasar da ta cigaba a duniya kasar da ta baiwa ilimi mahimmanci ne. A fito zahiri a mayarda hankali kan harkokin ilimi ba a dinga yin surutai ba. Kafin a cigaba sai an lura da lafiyar makarantu da yaran tun daga firamari har zuwa jami'a. Idan bada ilimi kayauta ba zai yiwu ba to menene gudunmawar iyaye da zasu kawo. Idan iyaye ba zasu iya biyan kudin makaranta ba to yaya gwamnati zata yi? Idan ilimi bai zauna da gindinsa ba babu wani abu na kasar da zai dore. Gwamnati ta fitar da kudi da yawa da tunane kan ilimi. Haka ma tunanen al'umma ya tattara ya koma kan ilimi.
Muddin ba'a gyara ilimi ba duk wata magana da ake yi tatsuniya ce kawai. Tsohon sifeton 'yansanda Ibrahim Kumasi mai wakiltar kungiyar tuntubar juna ta arewa yace basu ce kada a yi taron ba amma sun bada shawarwari. Na daya lokacin zabe ya karato domin haka a bari sai bayan zabe a yi taron. Na biyu yadda aka zabi wakilai ba'a yi kan ka'ida ba domin wani sashen kasar yana da rinjayen wakilai. Yace sun zo taron ne domin kada a ce su ne suka hana taron.
Taron ya baiwa kowane wakili minti uku ya bayyana ra'ayinsa.
Ga rahoton Saleh Shehu Ashaka.