Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Sabon Nau'in Kwayar Cutar Corona Samfurin XEC A Najeriya - Gwamnatin Tarayya


SYNEOS HEALTH-M&A/
SYNEOS HEALTH-M&A/

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi karin haske a kan cewa babu sabon nau'in kwayar cutar korona samfurin XEC, da aka gano a Austireliya da wasu kasashen Turai a Najeriya.

Jami'in ma'aikatar lafiya da walwalar jama'a, Kachollum Daju, ya tabbatar da cewa wasikar da aka aikewa shugabanin asibitoci da manyan daraktocinsu wacce sakonta ya bayyana a baya-bayan nan, an aikata ne domin gargadi amma ba don tada hankalin al'umma ba.

A ci gaba da jawabinsa, Daju yace an gano kwayar cutar korona samfurin XEC a kasashe 29, kuma saboda karatowar lokacin bukukuwan karshen shekara, lokacin da matafiya za su zo daga sassan duniya daban-daban, yana da muhimmanci ga asibitoci su aiwatar da matakan da za su tabbatar ba a shammaci kasar ba.

A wata wasika mai dauke da kwanan wata 5 ga watan Disamban da muke ciki, ma'aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya ta bukaci hukumomin lafiya su kaddamar da tsarin ko ta kwana a fadin asibitocinsu tare da sanya idanu sossai a kan marasa lafiya masu dauke da alamomin cutar korona.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG