A Najeriya, rahotanni na cewa har yanzu ana ci gaba da fuskantar matsalar karancin man fetir a wasu sassan kasar.
Wannan matsala ta sa mutane da dama sun shiga halin kuncin rayuwa wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Malam Bala Nayashi, wani mazaunin birnin Lokojaa jihar Kogi, ya ce karancin man ya jefa dumbin jama'a cikin kuncin rayuwa tare da takura masu.
A hirar da ya yi da Muryar Amurka, ya ce lamarin ya fi shafar masu tuka motocin haya da babura da ake kira Keke Napep ko Okada.
A cewarsa, tsadar mai din ya ta tilasta masu kara kudi yayin da su ma masu shiga ko hawan baburan suke kaurace masu.
A jihar Niger ma batun daya ne, Malam Muhammad Bello wani mai sana'ar tukin Keke Napep ya ce suna tafka asara sakamakon yadda lamarin karancin man fetur ke kara ta'azzara.
To ko me mahukunta ke cewa dangane da wannan lamari, saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Minna domin jin karin bayani.
Facebook Forum