Fadan dai ya kai fiye da wata daya ana yin sa da dakarun Iraki, da mayakan kurdawa da na ‘yan shi’a a dannawar da suke yi daga wajen garin zuwa cikinsa. Mayakan ISIS sun kame garin Mosul, gari mafi girma na biyu a Iraki, kusan fiye da shekaru 2 da suka gabata.
A wani rahotonta na baya-bayannan, ofishin bada agajin MDD ya fadi cewa mutane dubu sittin da shida da dari biyar da hamsin sun rasa matsugunnansu, mutane 14,000 daga cikinsu a makon da ya gabata su ka yi gudun hijira. Ta kuma yi gargadin cewa yayinda fadan ke kai ga wuraren dake da runtsi a birnin na Mosul, ta yiwu a sami karin mutanen dake tserewa daga birnin.
Kungiyar bada agajin Iraki da ake kira Red Crescent ta ce adadin masu gudun hijirar yanzu ya kai fiye da 85,000.