Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar China Zata Sake Kafa Tarihi Da Gadar Gilashi A Fadin Duniya


2232529 - G'day Australia
2232529 - G'day Australia

Kasar China ita ke da Gadar da tafi kowacce tsawo ta gilashi a duniya. Yanzu haka dai suna kara gina wata wadda ba’a taba ganin irin ta ba a fadin duniya. Ita dai gadar da ta taso daga wani tsuburi da ake kira Zhangjiajie zata kai tsawon murabba’in taku 1,400 da fadin taku 984.

Itadai gadar ta gilashi tafi kowacce komai a fadin duniya, kimanin tsawonta ya wuce tsawon gidan bene mai hawa 102, wanda ake kwatanta tsawon ta da tsawon karfen kasar Paris mai suna “Eiffel Tower” Ana dai sa ran za’a kammala wannan gadar a farkon wannan shekarar 2016 idan Allah ya kaimu, kana ana sa ran mutane 800 ne zasu fara hawan wannan gadar a lokaci daya, don tsallakawa daga bangare daya zuwa dayan.

Gwarzayen mutane ne kawai zasu iya tsallake gadar, batare da jin wani tsoro ba ko shakka. Don yadda take mutun zai iya tafiya akai kuma yana ganin nisan kasa, wanda hakan kan iya sa mutun ganin jiri.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG