Jami’in Hamas Taher Al-Nunu ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na afp a yau Talata cewar za’a saki wasu mata 4 da suke garkuwa dasu ran Asabar mai zuwa domin suma a sako musu Falasdinawa fursunoni, a karo na 2 na irin wannan sakin karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta.
Al-Nunu yace kungiyar ta gwagwarmayar Falasdinawa Musulmi zata saki matan Isra’ila 4 domin a sako mata rukuni na 2 na Falasdinawa fursunoni.
A Lahadin da ta gabata aka saki mata ‘yan Isra’ila 3 domin yin musayar Falasdinawa fursunoni 90, sakamakon fara amfani da ‘yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Isra’ila da Hamas.
A gabar farko ta yarjejeniyar, za’a sako da Yahudawa 33 da ake garkuwa dasu a Gaza domin yin musayar kimanin falasdinawa 1, 900.
A kwanaki 42 na farkon yarjejeniyar za a ga karuwar shigar kayan agaji sakamakon janyewar dakarun tsaron Isra’ila daga wasu yankuna na Gaza.
Har yanzu ana tattaunawa akan gaba ta 2 ta yarjejeniyar, inda kasashen Amurka da Masar da Qatar ke shiga tsakani.
Dandalin Mu Tattauna