Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yankewa Wani Dan Turkiyya Hukunci


Bankin Halk Na Turkiyya
Bankin Halk Na Turkiyya

Birnin Ankara tayi watsi da hukuncin daurin da Amurka tayi wani ma’aikacin Banki dan Turkiya sakamakon karya dokar takunkumin da data dora akan Iran.

Da yake magana da manema labarai a filin Jirgin sama na Istanbul a yau Juma’a bayan yanke hukuncin akan Mehmet Hakan Atilla, mataimakin babban daraktan bankin bada rance mallakin Turkiyya Halk Bank.

Shugaba Tayyep Erdogan yace ala’amarin wani bangare ne mai tsaho daga shirye shiryen makirci akan kasarsa, inda Erdogan din yayi gargadi akan dokokin kasa da kasa tsakaninsu da Amurka sun rasa madafa.

Ya kara da cewa, “idan dai har wannan itace fahimtar shari’a a wurin Amurka to hakika duniya na cikin hadari, babu wata fahimtar shari’a mai kama da wannan”.

A baya mai magana da yawun jam’iyyar AKP dake mulki Mahir Unal, kai tsaye ya zargi Amurka. Inda ya rubuta a twitter cewa, “Dalilin wannan shari’a a Amurka, yin katsalanda ne a harkokin cikin gidan Turkiya".

Shugaban Turkiyyar ya ci gaba da cewa, wannan shari’ar da aka yi keta dokar kasa da kasa ne mai cike da hatsari da barazana ga harkar shari'a. A bayyane yake a wannan hukunci bamu da wani abin fada akai don muna tababarsa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG