Najeriya ta yi tsit na wani dan lokaci domin karrama sadaukarwar sojojin da suka rasa rayukansu, yayin bikin tunawa da ‘yan mazan jiya na bana daya gudana a yau Laraba.
Najeriya ta cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka-saidai domin cigaba da dorewarta a matsayin dunkulalliyar kasa daruruwa koma dubban zaratan dakaru sun kwanta a kokarin kare kan iyakoki da diyaucin kasar.
Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ne ya wakilci Shugaba Bola Tinubu wanda ke halartar taron cigaba mai dorewa a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa, a bikin.
Baya ga Kashim Shettima, sauran mambobin majalisar ministocin Tinubu sun halarci bikin domin karrama dakarun da suka kwanta dama da iyalansu ta hanyar dora furan kallo, da gudanar da sauran al’adun soja ciki harda harba bindigogi sama.
Kowacce ranar 15 ga watan Janairu, rana ce da gwamnatin Najeriya ke gudanar da gangami na musamman don tunawa da tarin sojojin da suka rasa rayukansu a fagen yaki, ranar da ake yiwa lakabi da ranar tunawa da ‘yan mazan jiya wato Armed Forces Remembrance Day.
Dandalin Mu Tattauna