Amincewa da aiwatar da yarjejeniyar, yana nufin Habasha ta amince ta sakarwa Eritrea yankinta kana kuma zata mutunta hukuncin kotun kasa da kasa na shekarar 2002 da ya baiwa Eritrea ikon yankin Badme da kasashen biyu ke takaddama akai.
Shugaban Eritrea Isaias Afwerki ya sanar da wannan sabon labari ne a Asmara, a jawabinsa na shekara-shekara da akea tunawa da wadanda suka yi mutuwar shahada. Yace tawagar zata tattauna a kan ci gaba da aiwatar da shirin tsakanin kasashen biyu.
Daga bisani, shugaban ma’aikatar fadar firai ministan Habasha Fitsum Arega ya aike da sakon Twitter yana cewar, Firai ministan yana marhabi da tawagar Eritrea.
Facebook Forum