Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MASAR: Abdel Fattah El-Sissi Ya Fara Wa'adin Mulki Na Biyu


Shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sissi
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sissi

An rantsar da shugaban kasar Misira Abdel Fattah el-Sissi domin wa’adi mulki na biyu yau asabar, a gaban majalisar dokokin kasar, inda ya shaida masu cewa, yana daukar kansa a matsayin shugaban kasar dukan a’ummar kasar,da wadanda suka goyi bayansa da kuma wadanda basu goyi bayansa ba.

Kakakin majalisar dokoki Ali Abdel Aal ya gabatar da shugaba Sissi ga ‘yan majalisa ya kuma ayyana shi a hukamce, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar cikin watan Aprilu da hukumar zaben kasar ta aiwatar.

Sissi ya lashe kashi casa’in cikin dari na kuri’un da aka kada a zaben da aka kara tsakaninsa da wani kwararren mai zanen gine gine da ba sananne bane, da ya shiga takara ana dab da zabe. ‘Yan takara da dama fitattu ko dai sun janye, ko kuma an dakatar da su bisa hujjar cewa basu cancanci tsayawa takara ba.

Bayan daukar rantsuwa, Sissi ya bayyana cewa zai yi aiki tukuru domin gina kasa, da shata makomar da zata cimma burin al’ummar na zama kasar da taci gaba, da kafa tubalin ‘yanci da damokaradiya, da kuma maido da kasar Misira bisa turba da kima a kasashen duniya, abinda ya bijirewa kasar sabili da rikicin cikin gida.

Sissi ya kuma jadada cewa, al’ummar kasar Misira zasu hada hannu wajen yakar ayyukan ta’addanci har sai sun shawo kan matsalar baki daya.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG