Ya fara da bayyana takaicinsa game da irin kalamun da takwarorinsa na kudancin kasar keyi dangane da matsalar makiyaya.
Yace akwai wasu abokanan aikinsu na kudancin Najeriiya da sautari sukan yi furuci kafin su yi tunane. Yace matsalar yawon kiwo babbar matsala ce wadda ta dauko tarihi.
Yace a taronsu na farko na gwamnonin arewa sun yadda tilas ne su kirkiro da makiyaya a jihohinsu. Yace idan sun kirkiro makiyaya dole ne su jawo hankalin Fulani su rage yawan tafiya kiwo. Yakamata Fulani su canza salon yadda suke kiwon dabbobinsu.
Gwamnan ya cigaba da cewa a duniya gaba daya zama da dabbobin wuri daya ya fi a'ala. Yayi misalai da kasar Botswana wadda kasa ce karama amma ta yi suna wajen harkokin kiwo kuma irin na zamani. Yace ba yawo su keyi ba da dabbobinsu. Dabbobin suna ajiye amma makiyayi shi ne zai shuka ciyawar da dabbobin zasu ci kodayake wannan nada alaka da kimiya.
Gwamnan yace akwai farfasa guda a kasar China da ya gano irin ciyawar da za'a iya shukawa ko a hamada. Tuni aka je a ga irin abun da za'a iya dorawa akan ilimin domin alfanun jama'a.
Amma Ardo Salihu Abdullahi, makiyayi a jihar Bauchi ya yi tsokaci akan yadda suke ganin shirin tsugunar dasu wuri guda. Yace shi bafullatani ya saba yawo kuma abun da saniya zata ci ba kadan ba ne kuma suna bukatar ruwa.
Ga karin bayani.