Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Bitar Kawo Fahimtar Juna Tsakanin Masu Harkar Tsaro da 'Yan Jarida A Bauchi


Zauren da aka yi bitar tsaro a Bauchi
Zauren da aka yi bitar tsaro a Bauchi

Makasudin taron shi ne kautata fahimtar juna tsakanin masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro da kuma masu yayata bayanai a kafofi daban daban, wato 'yan jarida

Shugaban cibiyar Center for Crisis Communication, Commodor Yusuf Anas mai ritaya ya yi karin haske kan taron da suka shirya.

Yace cibiyarsu tana tattara bayanai akan rikice-rikice da akan samu a Najeriya kana kuma tana fito da wasu hanyoyi da ake ganin idan an yi anfani dasu za'a samu masalaha na shawo kan rikice-rikicen dake faruwa

Commodor Anas yace dalili ke nan suka shirya taron bitar. Yace wani lokaci akan samu rashin jituwa tsakanin jami'an tsaro da kuma 'yan jarida wajen tattara bayanai. Kungiyarsu ta ga ya kamata a kawo jamia'n tsaro da 'yan jarida domin a zauna a tattauna a gane matsalolin da suke fuskanta da yadda za'a magancesu.

Farfasa Shadrack Best na Jami'ar Jos ya gabatar da kasida akan hanyar da zata inganta bayanai a fannin tsaro. Yace idan an zo batun tsaro jami'an tsaro na ganin su kadai ne suke aikin, su kadai ne kuma suka fahimci aikin. Abun da suke son a sani shi ne hadin kan jami'an tsaro da 'yan jarida zai sa tsaro ya samu inganci a Najeriya.

Akan rashin samun bayanai da wuri daga jami'an tsaro da 'yan jarida ke fuskanta, shugaban 'yan jarida a jihar Bauchi Malam Aliyu Jibo, yace su hukumomin tsaro a duk lokacin da abu ya faru koda ma an samesu inda abun ya faru sai su ki bada bayani su ce su ba'a basu izinin yin magana ba.

Shi ma kakakin hukumar 'yansandan jihar Bauchi, Haruna Muhammad ya yi bayani game da rashin ba 'yan jarida bayanai a wasu lokuta. Yace kalubalen da suke samu daga 'yan jarida shi ne rashin hakuri. Ba sa ba jami'an tsaro lokaci su tattara bayanan da zasu basu. Kalubale na biyu ya ta'allaka ne da nasu jami'an da sai sun gudanar da bincike kafin su basu bayanan da zasu iya ba 'yan jarida.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG