Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Najeriya Sun Amince Da 'Yancin Cin Gashin Kan Bangaren Shari'a Da Majalisun Dokoki Na Jihohi


Taron Gwamnoni Arewacin Najeriya A Jihar Kaduna.
Taron Gwamnoni Arewacin Najeriya A Jihar Kaduna.

A can baya an zargi gwamnonin da yi kememe akan lamarin ne, saboda yadda suke yin kaka-gida da wadaka da kudaden kananan hukumomi, tare kuma da son karfin juya majalisun dokoki da bangaren shari’a don biyan bukatunsu na siyasa.

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ba da sanarwar amincewa da aiwatar da yarjejeniyar baiwa majalisu dokoki da bangaren shari’a na jihohi ‘yancin cin gashin kan su.

Gwamnonin sun cimma matsayar ne babban taronsu na 32 a Abuja, inda shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya bayyana matsayar ta su.

Kungiyar gwamnonin ta ce tsarin da za’a bi wajen aiwatar da yarjejeniyar ya sami amincewar kungiyar ma’aikatan shari’a da kuma kungiyar ma’aikatan majalisun dokoki, biyo bayan wani taro da aka gudanar, wanda ya hada har da kwamishinonin shari’a da na kudade na jihohin kasar, a ranar 25 ga wata Yunin wannan shekara.

An dade ana kai ruwa rana akan sha’anin na baiwa majalisun dokoki na jihohi da kuma bangaren shari’a na jihohin, har ma da kananan hukumomi 'yancin cin gashin kan su, lamarin da ya kai ga dogon yajin aikin ma’aikatan shari’a a fadin kasar a ‘yan kwanakin baya.

Masu fashin baki sun ta’allaka dambarwar da rashin kin yardar gwamnonin jihohi, duk kuwa da yake kundin tsarin mulki ne yayi tanadin baiwa wadannan sassa na gwamnati damar cin gashin kan su da tafiyar da kudadensu.

Karin bayani akan: gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, Nigeria, da Najeriya.

An zargi gwamnonin da yi kememe akan lamarin ne, saboda yadda suke yin kaka-gida da wadaka da kudaden kananan hukumomi, tare kuma da son karfin juya majalisun dokoki da bangaren shari’a don biyan bukatunsu na siyasa.

To sai dai gwamnonin sun sha musanta wadannan zarge-zargen.

Da alama kuma bangarorin biyu na majalisun dokoki da na shari’a a matakin jihohi za su fita daga kangin a halin yanzu, domin kuwa tuni da gwamnonin jihohin suka soma shirye-shiryen fara aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma ta ba su ‘yancin cin gashin kan su.

Yanzu haka gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya rattaba hannu akan kudurin ba su ‘yancin na su zuwa doka a farkon makon nan, yayin da a jihar Filato kuma, majalisar dokokin jihar ta zartar da kudurin dokar a ranar Laraba.

Yanzu dai ya rage ga kananan hukumomi su ma su sami na su ‘yancin cin gashin kai da sarrafa kudadensu, musamman la’akari da cewa su ne gwamnati mafi kusa da jama’a.

XS
SM
MD
LG