Batun ‘yanci ta fuskar kudade ga majalisun dokokin na jihohi da bangaren shari’a na jihohin da kuma kananan hukumomin Najeriya na cikin jerin abubuwan da majalisar dokoki ta Najeriya ta shigar sassan da aka yiwa kwaskwarima a cikin kundin tsarin mulkin kasar a kwanakin baya.
An sake tada wannan batu ne da nufin ganin ba kananan hukumomi ‘yancin samun kudadensu kai tsaye domin su iya gudanar da ayyuka ga al’ummominsu, bisa la’akari da cewa, wadansu kananan hukumomi sun zama kufai.
Masu kula da lamura na cewa, rike kudaden kananan hukumomi da aka yi shine ya haifar da talaucin da ake fama da shi a Najeriya da har yanzu aka kasa sanin hanyar fita daga ciki. Bisa ga cewarsu, kasancewa akwai dokoki da sharuddan amfani da kudaden, babu hujjar ba gwamnonin jihohi ikon kasafta kudadaden kananan hukumoni.
Bisa ga tsarin da ake bi yanzu dai, ya ana ba gwamnoni kudaden kananan hukumomi kafin daga baya su yanke hukumci kan yadda za a kasafta su.
Masu kula da lamuran sunce babu shakka majalisasun dokoki na jihohi suna da muhimmiyar rawar takawa wajen tabbatar da ‘yancin kudaden kanan hukumomi.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Facebook Forum