Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnoni da Sanatoci Suna Kallon Kallo


Gwamnan Jigawa da Kano
Gwamnan Jigawa da Kano

Yayin da zaben shekarar 2015 ke karatowa wasu gwamnoni da sanatoci a jihohi da dama suna kokarin su sake mukamai

Yayin da zaben shekarar 2015 ke dada karatowa wasu gwamnoni da zasu kare wa'adinsu suna kwadayin su zama sanatoci su shiga majalisar dattawa wadda tuni ta fara zama matattarar tsofofin gwamnoni.

Burin wasu gwamnoni su zama sanatoci ya fara kawo sabani tsakaninsu da sanatocin dake ci yanzu. Sai dai da yawa cikin gwamnonin idan an tambayesu sai su musanta maganar. Misali a jihar Kebbi gwamnan jihar na son zama sanata abun da yasa mutanen sanatan dake ci yanzu suna cewa a basu gwamna su kuma su bada sanato. Amma Alhaji Ibrahim Musa Argungu mai ba gwamnan shawara a harkokin labarai cewa ya yi gwamnan har yanzu bai fito ya ce zai yi takarar sanata ba.

A jihar Neja har an fara samun rashin jituwa tsakanin sanato mai ci yanzu da gwamnan. Kwanan nan aka ji sanaton yana cacakar gwamnatin Neja. Ya ce idan ba an dawo an bi shugaban kasa yadda ya kamata ba talaka ne zai sha wuya. Gwamnatin jihar Neja da gwamnan talauci ba zai shafesu ba. Ya ce akwai talauci da wulakanci a jihar irin wadanda ba'a taba gani ba a jihar.

A wani abu kamar mayarda martani kwamishanan aiki na jihar Neja Alhaji Muazu ya ce duk wanda ya ce gwamnatin jihar bata aikin komi to bai san abun dake faruwa a jihar ba ne. Ya ce kila baya zuwa gida ganin mutanensa. Irin 'yan siyasan nan ne masu zama din dain din a Abuja. Ya ce duk wanda ya zo garin Minna ya san ta canza. Da aka tambayeshi ko gwamnan zai tsaya takarar sanata sai ya ce har yanzu bai fito ya ce zai tsaya ba. Ayyukan jihar ne gwamnan ya sa a gaba.

A jihar Jigawa sanatocin jihar sun kauracewa taron sanatoci da jam'iyyar PDP ta kira domin goyon bayan gwamnansu. Haka ma Kano babu irin wannan barakar domin kawo yanzu gwamna Kwankwaso bai ce zai tsaya takarar sanata ba duk da cewa yana zango karshe ne.

A jihohin Bauchi da Katsina babu baraka domin babu daya da ya fitar da maitarsa fili. A Binuwai kuwa gwamnan da sanaton da yake so ya ture sun soma takunsaka. Sai dai abun da wuya domin wanda gwamnan ke neman turewa sananne ne a faggen siyasa.

A jihar Abia an yi taron fahimtar juna inda sanata mai ci yanzu zata dawo ta yi takarar gwamna shi kuma gwamnan mai barin gado ya yi takarar sanata. Haka ma lamarin yake a jihar Filato.

A jihar Akwa Ibom lamarin ya sha bambam da abun dake faruwa a Abia da Filato. Akwai rashin jituwa tsakanin gwamnan da sanatan da yake so ya maye gurbinsa. Gwamnan Delta ma yana son ya zama sanata. Haka ma labarin yake a jihar Cross Rivers.

Ga cikakken bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG