Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Da Dama Suka Hallaka Sakamakon Harin Guba A Syria


Fararen hula da dama sun mutu sannan wasu sun samu raunuka a arewacin Siriya, a wani harin gubar iska, wanda masu lura da al'amura da jami'an diflomasiyya da kwararru ke zargin sojojin gwamnati masu biyayya ga Shugaba Bashar al-Assad kuma masu alaka da Rasha da aikatawa.

Wata hadakar kungiyoyin agaji na yammacin duniya ta fadi tun farko a jiya Talata cewa adadin mutanen da su ka mutu a garin Khan Sheikhoun da ke lardin Idlib sun kai 100 yayin da kuma wasu 350 su ka dimauta.

Kasar Rasha dai ta fito karara ta nesanta kanta daga wannan harin. Ita ma gwamnatin Siriya ta sha karyata zirgin amfani da makaman guba kan farar hula a tsawon yakin da aka kwashe shekaru 6 ana yi.

Kwamitin Sulhu na majalisar dinkin duniya zai tabo batun wannan harin da aka kai a Khan Sheikhoun a wani zama na gaggawa ranar Laraba da safe.

Daga can kudancin kasar kuma, masu saka ido na kungiyar kare hakkin dan adam a Siriya ta ce mutane akalla 25, galibinsu mata da yara sun halaka jiya Talata a wani harin jirgin sama da aka kai a wurare da dama a gabashin birnin Dimashku.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG