Najeriya tace ta fara tattaunawa da kungiyar Boko haram da ake dorawa alhakin kashe daruruwan mutane a hare haren boma bomai da harbe harben bindiga cikin watanni goma sha takwas da suka shige.
Majiyun siyasa da na diplomasiya da suka bukaci a saya sunayensu, sun ce masu shiga tsakani suna kai sakonni tsakanin kungiyar da gwamnati.
Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa, kungiyar Boko Haram ta bukaci a saki dukan membobinta da ake tsare da su a gidajen yari kafin ta daina kai hare hare. Gwamnati tana nazarin wannan tayin.
Shugaba Goodluck Jonathan yana fuskantar matsin lamba na neman dawo da zaman lafiya a arewacin kasar inda kungiyar Boko Haram take kai hare hare akasari kan jami’an ‘yan sanda da na gwamnati da kuma sauran hukumomi.