Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Shirya Gudanar Da Bincike A Matatar Man Kasar


Matatar Mai
Matatar Mai

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta bayyana shirin gudanar da bincike a matatar hadin gwiwar kasar da China wato SORAZ domin tantance abubuwan da suka wakana shekaru sama da 10 bayan kaddamar da ayyukanta

Wannan yunkuri na zuwa a wani lokacin da aka fara fuskantar kace-nace tsakanin matatar ta SORAZ da kamfanin dillancin man fetur wato SONIDEP dangane da matsalar karancin man da aka yi fama da shi a karshen watan Disamba 2024 a wasu jihohin kasar.

A taron majalissar ministoci na baya bayan nan ne ministan man fetur Dr. Sahabi Oumarou ya sanar da shirin bayar da kwangila wa wata cibiyar da za ta binciki matatar SORAZ wacce aka jima ma’aikata da masu kula da harkokin man fetur na korafi game da yadda ake tafiyar da lamuranta daga bangaren jami’ai ‘yan Nijar ko daga bangaren ‘yan China da ke da ruwa da tsaki.

Matakin da kwararru a kan sha’anin ma’adinai irinsu Mahamadou Tchiroma Aissamisuka ya yi na’am da shi.

Tun a ranakun farko da Nijar ta fara hakar manta wasu ‘yan kasar ke korafi a game da tsadar litar a gidajen mai lamarin da ke shafar farashin kayayakin abinci, sufuri da dai sauransu.

A tsawon shekarun da harkokin mai ke karkashin ikon ‘yan siyasa gwamnatin kasar ta yi buris da bukatar rage farashi kafin gwamnatin mulkin sojan ta CNSP ta samar da rangwame kan kowace litar a bara.

Kasancewar sha’anin man fetur kamar sauran albarkatun karkashin kasa fanni ne da ke zama tamkar wani abin gagara da ya sa kwararru gargadin hukumomi a kan bukatar daukan wasu matakan riga kafi.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Gwamnatin Nijar Ta Shirya Gudanar Da Bincike A Matatar Man Kasar.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG