Mukaddashin gwamnan, wanda ya ziyarci gwamnan a inda ake masa jinya a Amurka, yace Mr. Suntai yana samun sauki, kuma sun gaisa sosai har ma ya gode masa a kan yadda yake rike ragamar harkokin jihar Taraba.
Alhaji Garba Umar ya ce, "...daga gani na (Suntai) ya tashi, muka kama hannun juna yana ce mini ya gode, ya gode. Yayi murmushi, aka kuma dauke mu a hoto, wanda aka nuna a duniya kowa ya gani."
Mukaddashin gwamnan yace a bayan nan babu wata maganar da suka yi.
A kan ko yaushe gwamna Danbaba Suntai zai komo Jalingo, mukaddashin gwamnan yace ,likitocin da suke duba shi ne zasu yanke wannan shawara.
Akwai jita-jita da yawa cewar ana wani yunkurin dauko gwamnan a maida shi Najeriya, duk da cewa bai kammala warkewa ba.
Ga cikakken rahoton da Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko daga Abuja, kan tattaunawar da shi mukaddashin gwamna Alhaji Garba Umar, yayi da 'yan jarida, da kuma iri n martanin da masu sharhi suka mayar kan batun.