Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Yawan Matasan Dake Cikin Shirin N-Power Ba Su San Wuraren Aikinsu Ba


Shirin samarwa matasa aiki a Najeriya
Shirin samarwa matasa aiki a Najeriya

Shirin gwamnatin tarayyar Najeriya na samar wa matasa aiki wanda ake yiwa lakabi da N-Power har yanzu na fuskantar matsaloli.

A watan jiya ne gwamnatin tarayya ta fitar da jerin sunayen matasa dubu 200, wanda tace sun sami nasarar shiga kashin farko na shirin da gwamnati ta yi don tallafawa matasa marasa aikin yi.

Kwanaki biyar ke nan tunda da shirin N-Power ya fara aiki a Najeriya, sai dai kuma har yanzu fara shirin gadan-gadan bai kankama ba. A cewar wasu matasan da suka sami nasarar shiga cikin shirin har yanzu basu fara aikin ba.

Kungiyar kwadago ta Najeriya tace bata gamsu da wannan shiri ba, a cewar shugaban kungiyar duk da yake ba wannan shiri bane zai shawo kan matsalar rashin aikin yi na din din din a Najeriya ba, kuma ya bayar da shawarar gyara masana’antu domin sune zasu iya tanadar da ayyukanyi.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:29 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG