Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Allah Ya Yi Wa Wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdul'aziz Rasuwa


Ibrahim Abdul'aziz Yola
Ibrahim Abdul'aziz Yola

Allah ya yi wa wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz rasuwa yau jumma'a sakamakon mummunan hatsarin mota.

Ibrahim Abdul'ziz wanda kafin rasuwarsa ya ke daukowa Sashen Hausa rahotanni daga jihohin Adamawa da Taraba, ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyarsu ta komawa gida daga Bauchi inda suke tafi daurin auren abokinsa tare da yayansa Mai Unguwa.

Abdul'aziz yana daya daga cikin hazikan wakilan Sashen Hausa da banda rahotanni, loto-loto yake jagorantar gabatar da shirye shirye na musamman a Sashen Hausa.

Ibrahim Abdul'aziz Yola
Ibrahim Abdul'aziz Yola

Abdul'ziz ya kware a dauko rahotannin da suka shafi rayuwar talaka ta yau da harkokin siyasa da kuma harkokin tsaro.

gwamnatocin-binuwai-da-taraba-sun-dau-matakan-kawo-karshen-rikici-a-tsakaninsu

jam-iyyar-pdp-ta-lashe-adamawa

a-jihar-taraba-anyi-cincirindo-wajen-ganin-likita-kyauta

apc-ta-kare-dan-takarar-gwamnan-taraba-kan-zargin-wawurar-naira-miliyan-

Kafin rasuwarsa, Abdul'ziz ya shirya muhawara ta musamman kan siyasa da harkokin mulkin Najeriya da ake gabatarwa a shirin Tsaka Mai Wuya ranar Talata.

Banda Muryar Amurka, Ibrahim Abdul'aziz yana kuma daukowa wadansu kafofin larabai da dama labarai da suka hada da Daily Trust, Premium Times, allAfrica, newscrescue da sauransu.

we-executed-10-christians-to-avenge-our-leaders-killed-in-nigeria-isis-claims-in-new-video

gunmen-kill-two-in-adamawa-village

terrorists-abduct-nigerian-police-dpo

Ibrahim Abdul'aziz Yola da abokansa Fulani
Ibrahim Abdul'aziz Yola da abokansa Fulani

Saurari shirin A Bari Ya Huce na musamman ranar asabar inda zamu karrama marigayi Ibrahim Abdul'aziz Yola.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG