Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Tallafawa Da 'Yan banga Da Babura 730 Domin Tunkarar Barayin Daji


Gwamnan jihar Kebbi yayin da yake raba babura ga jami'an tsaron banga domin taimakawa a shawo kan matsalar tsaro
Gwamnan jihar Kebbi yayin da yake raba babura ga jami'an tsaron banga domin taimakawa a shawo kan matsalar tsaro

Gwamnatin jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta samar da babura dari bakwai da talatin, domin rabawa jami'ansa kai na banga, domin su rika taimakawa jami'an tsaro na hukuma wajen sintiri don yaki da matsalar rashin tsaro.

Tun bayan da gwamnonin jihohin arewa maso yamma suka hadu, tare da daukar kudurin yin aiki tare don shawo kan matsalar rashin tsaro, har yanzu ana samun rahotannin kai hare-hare a wasu jihohi, abin da ke nuna tsugunne bata kare.

To sai dai a kamar yadda mahukunta ke cewa, suna kokarin magance matsalar ta hanyar daukar matakai daban-daban.

Jihar Kebbi na daya daga cikin wuraren da bayanai ke nuna jami'an sa kai na banga na bayar da gagarumar gudunmuwa ga sha'anin tsaro.

Shugaban kungiyar banga na jihar, Sanusi Ibrahim Geza, ya tabbatar da cewa, jami'ansu sun hallaka masu satar mutane a karamar hukumar Ngaski da Danko Wasagu, da kuma wani jagoran masu garkuwa da mutane a yankin Bunza da Kalgo mai suna Dogo Oro.

Bisa la'akari da haka ne, ya sa gwamnatin jihar ta samar da babura 730, domin rabawa jami'an na banga, baya ga motoci da gwamnatin ta baiwa jami'an tsaro kwanannan.

Baburan da gwamnatin Jihar Kebbi ta rabawa 'yan banga domin samar da tsaro
Baburan da gwamnatin Jihar Kebbi ta rabawa 'yan banga domin samar da tsaro

Gwamnan jihar Kebbi, Dokta Nasir Idris, ya bayyana cewa an samar da baburan ne domin 'yan banga su rika taimakawa jami'an tsaro na hukuma wajen samar da tsaron jihar ta Kebbi.

Shugban kungiyar ta banga a jihar Sanusi Ibrahim Geza ya ce samar da babran faduwa ce ta zo daidai da zama, domin da ma baburan ne su ke bukata kuma sun samu wadanda ma suka fi wadanda barayin daji ke amfani da su.

Ko bayan baburan, shugaban kungiyar banga ya ce an samar musu bindigogi da za su yi aiki da su wadanda yanzu haka suna ajiye a hannun jami'an 'yan sanda.

Masana tsaro kamar Detective Awal Bala Dirimin-Iya na ganin wannan wani kyakkyawan mataki ne na samar da tsaro, domin jami'an tsaro na gwamnati ba su da yawan da zasu iya kai ko'ina, kuma jami'an banga su ne suka fi sanin sako da lungu na jihar.

Duba da yadda al'amurra ke tafiya a wasu jihohi, inda siyasa ke yin kane-kane cikin al’amuran, masu lura da al’amuran yau da kullum na karfafa fatar kar a saka siyasa cikin lamarin ta yadda zai amfanin jama'ar da aka yi domin su.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG