Wasu daga cikin yara dalibai da kuma iyayensu da suka fito gangamin sun bayyana bakin cikin su musamman a kan yadda lamarin ke shafar yanci ‘ya’yan talakawa da basu da wata mafita kuma daga karshe yakan kai su ga hallaka.
Matan sun fito da safiyar yau talata duk da ruwan sama da aka tashi da shi, amma bai hana matan fitowa ba sai dai jami’an ‘yan sanda suka hana su.
Daruruwan mata ne suke fito tattakin daga Lugard Road, zuwa gidan gwamnati zuwa majalisar dokoki kana zuwa majalisar mai martaba sarkin Kano. Kungiyar tsaffin daliban kwalejin mata dake St. Louis, ta jihar Kano ce ta shirya tattakin.
Mata da dama sun bayyana ra’ayoyinsu akan rashin samun nasarar wannan yunkuri nasu musamman ganin yadda gwamnati ce da kanta ta hana, wanda a cewar su, yunkuri ne da ya kamata a ce gwamnati da kanta ta marawa baya domin kare al’umma daga miyagun ayyuka.
Daraktan labaru na gwamnan jihar Kano Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana cewa gwamnatin ta dauki wadannan matakai ne a sakamakon dalilan tsaro musamman idan aka yi la’akari da yanayin da kasar ke ciki. Ya kuma kara da cewa hanya mafi dacewa hanya mafi dacewa ita ce gwamnati ta gayyace su domin tattaunawa a kan lamari.
Masana kiwon lafiya na ci gaba da bayyana irin barazanar da fyade ke yiwa al’umma musamman masu tasowa a dai dai lopkacin da al’kalumman yaran da lamarin ya shafa suke karuwa.
Domin cikakken bayani, saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari a nan.
Facebook Forum