Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin Fadar Gwamnatin Najeriya Ya Bayyana Muhimancin Ziyartar Shugaba Buhari


A yayin da wasu kungiyoyin sa kai na Najeriya da ‘yan siyasa ke shirin zaman durshan cewar sai shugaba Muhammadu Buhari ya dawo akan karagar mulkinsa cikin kwanaki Talatin, kokuma su dukufa wajan fafutukar tsige shi daga kujerarsa ta shugaban kasa,

Wasu gwamnoni da shugabannin jam’iyyar APC sun ziyarci shugaban a birnin London.Shugabanin sun ziyaci shugaba Muhammadu Buhari a birnin London inda yake jiyya kuma sun yaba da koshin lafiyarsa tare da ba ‘yan Najeriya tabbacin dawowar shugaban nan ba da jimawa ba.

A kan wannan sanarwar da fadar gwamnatin Najeriyar ta bayar dangane da wannan ziyara yasa wakilin sahsen Hausa na muryar Amurka, Umar Faruk Musa ya sami zantawa da Malam Garba Shehu, kakaki a fadar gwamnatin Najeriya, domin jin muhimmancin ziyarar.

Da yake bayani, kakakin fadar gwamnatin ya bayyana cewa daya daga cikin muhimmancin ziyarar shine kwantarwa da jama’a hankali musamman akan yadda ake ta cece kuce da kuma zancen daukar wasu mataka domin tsige shugaban.

Bayan hotunan da aka nuna na shugaban a shafukan yanar gizo, da alamu ‘yan Najeriya sun ganawa domin ganewa idanusu kasancewar yadda shugaban ya sami koshin lafiya.

Daga Abuja Umar Faruk Musa nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG