Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Buhari ta kammala shirin kubutar da al'ummar Najeriya daga fatara da talauci


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

A cikin kasafin kudin bana na Najeriya gwamnatin Shugaba Buhari zata kashe nera biliyan 500 wa akalla 'yan Najeriya fiye da miliyan takwas a hanyoyi daban daban domin su samu dogaro ga kansu, wannan kuma soma tabi ne domin akwai wasu tsare-tsaren da gwamnatin zata aiwatar a kasafin kudin wannan shekarar.

A cikin sanarwar da ta fito daga ofishin mai taimakawa shugaban kasa akan harkokin labarai, gwamnatin Buhari zata kashe nera biliyan dari biyar domin taimakawa a fannoni daban daban da zummar yakar fatara da talauci.

Ga yadda sanarwar tace gwamnatin Buhari zata kashe nera biliyan dari biyar a wannan shekarar wa talakawa:

1. Kowane wata gwamnati zata ba mutane miliyan daya da suka fi kowa talauci a kasar, kowannensu nera dubu biyar har na tsawon watanni goma sha biyu. Tuni gwamnati tayi tanadin nera biliyan 68.7

2. 'Yan kasuwa mata da maza da masu aikin hannu da kananan manoma zasu sami lamuni ba tare da biyan kudin ruwa ba. Akalla mutane miliyan daya da dubu dari bakwai da sittin ne zasu ci gajiyar wannan tallafin. Dangane da wannan shirin gwamnati tayi tanadin kudi nera biliyan 140.3

3. Wadanda suka kammala karatun jami'a dubu dari biyar da basu da aikin yi zasu samu horo akan fannoni daban daban. Lokacin da suke samun horon za'a dinga biyansu alawus kama daga N23,000 zuwa N30,000 kowane wata. Bayan sun kammala horon za'a tura wasunsu su yi aikin koyaswa, aikin kiwon lafiya da wasu ayyukan taimako. Za'a kuma basu naurorin zamani da zasu taimakesu wurin ayyukansu da ma na karan kansu. Za'a kuma horas da masu aikin hannu su dubu dari daya. Duka wadannan shirye siryen zasu lakume nera biliyan 191.1 da gwamnati ta riga tayi tanadi a kasafin kudin bana.

4. Akalla 'yan makarantun firamare su miliyan biyar da dubu dari biyar ne a jihohi 18 daga shiyoyi shida na fuskar siyasa za'a dinga ciyar dasu na tsawon kwanaki 200 a karkashin wani shirin "Ciyar da 'Yan Makaranta" . Gwamnati tayi tanadin nera biliyan 93.5

5.Dalibai dubu dari daya dake makarantun gaba da sakandare da suke koyan ilimin kimiya da fasaha da aikin injiniya da lissafi da ilimin koyaswa zasu ci gajiyar nera biliyan 5.8 da gwamnatin ta tanadawa shirin ilimi.

Idan aka hada duk wadannan kudaden gwamnati zata kashewa mutane fiye da miliyan 8 zunzurutun kadaden nera biliyan 500 saboda ragewa 'yan Najeriya talauci da fatara.

Wannan mataki da gwamnati ta dauka zai rage radadin tsadar man fetur da aka kara ma farashi makon jiya.

Baicin wannan shirin da gwamnati tayi gwamnatin zata kirkiro ayyukan yi sanadiyar gine-ginen gidaje da hanyoyi da gwamnatin zata fara aiwatarwa nan ba dadewa ba.

Daga lokaci zuwa lokaci gwamnatin Buhari zata dinga fito da shirye-shiryen da zasu taimakawa jama'a fita daga talauci.

XS
SM
MD
LG