Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Kyautata Ma Bangaren ‘Yansanda


Wasu 'yansandan Najeriya a bakin aiki
Wasu 'yansandan Najeriya a bakin aiki

An sake yin alkawarin kyautata ma 'yansanda a Najeriya

Nan ba da jimawa ba Najeriya za ta kyautata bangaren ‘yansanda ganin muhimmancin bangaren da kuma halin da ‘yansandan ke ciki, a cewar Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai Mai Kula Da Bangaren ‘Yansanda, Alhaji Halliru Dauda Jika.

Da yak e bayani ga wakilinmu a Bauchi Abdulwahab Muhammed, Alhaji Jika ya ce daga cikin aikin kyautata bangaren na ‘yansanda har da daukar sabbin jami’an ‘yansandan ta hanyar yanar “internet” ba tare da an sha wahala ko kuma wata matsala ba.

Aljhaji Jika ya kuma ce za a raba aikin daukar ‘yansandan ne a duk fadin kananan hukumomin Najeriya ta yadda kowane bangaren zai san ana yi da shi.

Ga wakilnmu Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:49 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG