Wani yace sun dade suna jiran janye tallafin domin sun gaji da gwamnatoci daban daban suna fada masu kasar na hasarar biliyoyin nera da yakamata a yiwa mutane aiki dasu saboda tallafin farashen man fetur.
Tunda yanzu ana kukan rashin kudi kuma duk da talllafin babu mai mai saukin kudi saboda haka a cire tallafin shi ya fi alheri.
Shi ma Muhammad Ismail yace a zahirin gaskiya ya ji dadi da cire tallafin domin dama ba talakawa ake tallafawa ba. Wasu masu kudi ke cin gajiyarsa.
Ga masana tattalin arziki irinsu Ado Ibrahim Song malami a kwalajin kimiya da fasaha ta jihar Adamawa yace tun daga mulkin Babangida aka sha yin hakan amma babu abun da ya fito na alfanu ga talaka. Abacha ne kawai ya yi amma ya kafa PTF wadda Buhari ya shugabanta ta dinga ginawa kasar hanyoyi.Talakawa sun ga anfanunsa.
Ibrahim Song yace abun da gwamnatin Buhari ta yi yanzu daidai ne kuma zai taimaka 'yan kasar su dawo da hankulansu su fuskanci gaskiyar rayuwa. Yakamat 'yan kasar su sani shugaban kasa ya dauki gyaran hanyoyin Najeriya gaba daya da an kwashi shekaru 30 ba'a gyarasu ba kuma babu kudin amma kuma an sa a kasafin kudi. Dole ne a cire tallafin mai domin a samu kudin gyara hanyoyi.
Dangane da barazanar shiga zanga zanga da kungiyar kwadago ta yi Alhaji Uba Dan Arewa yace dole 'yan kwadago su hakura yanzu. Yace sun yaki gwamnatin Jonathan ta tafi balle kungiyar kwadago.Yace me yasa lokacin da ake sayen galan daya na mai nera dubu uku kungiyar kwadago bata tashi ta yi zanga zanga ba?
Ga karin bayani.